Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya ce ta samar da bayanan sirri (intelligence) da suka kai ga hare-haren sama da Amurka ta kai kan ‘yan ta’adda, tare da amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin a aiwatar da su. Tuggar ya fadi hakan ne a Jumma’a, 26 ga Disamba, 2025 da misalin 10:27 na safe, yayin wata hira a tashar Channels Television.
A cewarsa, hare-haren sun kasance sakamakon haɗin gwiwar tsaro da ke gudana tsakanin Najeriya da Amurka, ba tare da wata alaka da addini ba. Ya ce ya tattauna tsawon minti 19 da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, kafin ya gana da Shugaba Tinubu domin bayar da sahalewa, inda suka amince a fitar da bayanai da za su nuna cewa yaki da ta’addanci ne kawai ake yi.
Tuggar ya kara da cewa wannan mataki ya tabbatar da kudurin gwamnatin Tinubu na aiki da dukkan kasashen da ke da niyyar kawo karshen ta’addanci, ko da wane addini ko yankin da lamarin ya shafa. Ya jaddada cewa manufar aikin ita ce kare rayukan fararen hula, yayin da Amurka ta tabbatar da kai harin ne bisa bayanan da Najeriya ta bayar, a wani yunkuri na raunana kungiyoyin ta’addanci da ke addabar wasu sassan kasar.

