Wani ɗan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki, ya tayar ƙura a zaman majalisar ranar Laraba, 17 ga Disamba, 2025, inda ya bayyana cewa dokokin haraji da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da su ba su yi daidai da abin da aka wallafa a cikin kundin dokokin gwamnati ba. Dasuki ya ce wasu sassa na dokokin sun sha bamban da sigar da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka amince da ita bayan da aka yi daidaito a kansu.
Da yake magana a ƙarƙashin tanadin kare haƙƙin ‘yan majalisa, Dasuki ya ce ya duba takardun zaman majalisar da kuri’un da aka kaɗa, tare da kwatanta su da kundin dokokin da aka fitar, inda ya gano canje-canje masu yawa. Ya jaddada cewa a matsayinsa na ɗan majalisa da ya halarci zaman kuma ya kaɗa ƙuri’a, abin da aka gabatar wa ‘yan Najeriya a halin yanzu ba shi ne abin da aka amince da shi ba.
Ɗan majalisar ya bayyana lamarin a matsayin keta Kundin Tsarin Mulki, yana mai kira da a mayar da dokokin gaban Kwamitin Majalisa baki ɗaya domin a yi gyare-gyaren da suka dace. Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya tabbatar wa ‘yan majalisar cewa za a binciki lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace domin kare muradun ƙasa.

