Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa Hukumar EFCC ta aika masa da takardar gayyata zuwa ofishinta, kuma ya amince zai je ranar Litinin mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, yana mai cewa ya riga ya sanar da hukumar cewa zai amsa gayyatar.
Wannan na zuwa ne bayan rahoton cewa jami’an tsaro sun ƙwace fasfonsa a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe jim kaɗan bayan dawowarsa daga Masar.
Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya wallafa cewa jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama shi bayan isowarsa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
Da yake karin haske, El-Rufai ya ce jami’an DSS ne suka tare shi a filin jirgi suna neman ya bi su ofisinsu, amma ya nemi a nuna masa takardar gayyata.
Ya ce babu wata doka da ta ba da damar tsare mutum ba tare da takarda ba, tare da zargin cewa ana matsa wa ’yan adawa lamba ta hanyar kama su da sunan binciken rashawa.

