Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) reshen Ilorin ta kama mutane 10 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ilorin–Ogbomosho na Jihar Kwara. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Litinin.
EFCC ta ce an kama mutanen ne a ranar Lahadi, 1 ga Fabrairu 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa doka ba a wasu sassan jihohin Kwara da Oyo. An gudanar da kamen ne ta hanyar wani shiri na musamman da ya shafi tono da safarar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda aka kama sun haɗa da direbobin manyan motoci tara da kuma mutum guda mai rakiya, inda aka same su suna jigilar ma’adanai irin su lithium, tin da lepidolite ba tare da lasisi ko izini ba. EFCC ta ce an kwace motocin da ke ɗauke da ma’adanain, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu bayan kammala bincike.

