Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa ana tilasta wa wasu ’yan siyasa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki ko su ci gaba da zama a cikinta.
Ya bayyana hakan ne yayin da harkokin siyasa ke ƙara zafi gabanin babban zaɓen 2027.
El-Rufai, wanda ya tsananta sukar gwamnatin Bola Tinubu a baya-bayan nan, ya ce duk da ba a kama shi ba, an kama wasu na kusa da shi.
A wata tattaunawa da BBC, ya ce an kama mutum huɗu da suka yi aiki tare a Kaduna, yana mai cewa watakila shi ma lokaci ne kawai.

