Wata gobara ta tashi a ranar Talata inda ta ƙone tantuna 76 na ‘yan gudun hijira daga Jihar Borno a ƙauyen Ngamma, Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe. Gobarar, wadda ta tashi da rana, ta bazu cikin sauri kafin a samu nasarar shawo kanta.
Rahotanni sun ce mutum ɗaya ya jikkata aka kai shi asibiti, yayin da iyalai da dama suka rasa matsugunansu gaba ɗaya. Gobarar ta kuma lalata dabbobi, kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin rayuwa na waɗanda abin ya shafa.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA), Dr. Mohammed Goje, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana shi a matsayin abin takaici. Ya ce an kammala tantance asarar domin raba kayan agaji ga waɗanda gobarar ta rutsa da su, yayin da har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

