Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin haɗa kan dukkan ƴan siyasar jihar tare da yin gargadi kan abin da ya kira siyasar mutuwa ko rai. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron addu’a da karatun Alƙur’ani na musamman da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, inda mahaddata 4,444 suka halarta.
Gwamnan ya ce halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, a wasu shirye-shiryen gwamnati alama ce da ke nuna ana samun fahimtar juna a tsakanin shugabannin siyasa. Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa rikicin masarautar Kano zai samu mafita cikin lumana sakamakon addu’o’in da aka gudanar.
Abba Yusuf ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo karshen daba a jihar, yana mai cewa matasan da ke shiga irin wannan hali ‘ya’yan kasa ne da ya kamata su bayar da gudunmawa mai amfani. A nasa bangaren, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bukaci jama’a su ci gaba da addu’a domin zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.

