Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ware sama da Naira miliyan 800 domin shirye-shiryen tallafawa al’ummomin da ba ’yan asalin jihar ba, ciki har da Igbo, Hausawa, Yarbawa da mutanen Niger Delta. Ya yi wannan bayani ne yayin bikin Igbo Unity Day a Uyo, inda ya tabbatar da cewa gwamnati na kokarin gina jihar da haɗin kan duk kabilu.
Gwamnan ya jaddada cewa Akwa Ibom ta zama wurin haɗuwar al’adu daban-daban saboda yadda gwamnatinsa ke goyon bayan zaman lafiya. Ya yaba wa al’ummar Igbo kan yadda suka taka muhimmiyar rawa wajen kasuwanci da ci gaban jihar, yana mai cewa da dama daga cikinsu an haife su a Akwa Ibom kuma sun kafa nasu kasuwancin a nan. Ya kara da cewa shugabancin Igbo na jihar ya kasance ginshiƙi wajen samar da zaman lafiya da hadin kai.
A yayin taron, Ohaneze Ndi Igbo sun girmama Gwamna Eno tare da bayyana goyon bayansu ga takararsa da ta shugaban kasa Bola Tinubu da Sanata Godswill Akpabio a 2027. Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da hada kai da kabilu daga waje muddin suna bin doka kuma suna gudanar da sana’o’insu cikin lumana.
Shugaban Ohaneze Ndi Igbo na jihar, Kayceey Chidiadi, ya yaba wa gwamnan kan yadda ya bai wa al’ummar Igbo dama a manyan mukaman gwamnati, abin da ya ce ba a taba yi musu ba tun bayan kirkiro jihar. Ya bayyana cewa irin wannan siyasar hada kan jama’a ta sa al’ummomin da ke zaune a jihar ke jin kansu a matsayin ’yan gida na gaskiya.

