Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan janyewar jami’an ‘yan sanda daga jerin gwanon bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a jihar.
A jawabinsa yayin bikin, Yusuf ya zargi kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, da nuna son rai da siyasa, yana mai kiran matakin da “abin kunya ne” da kuma saba wa tsarin doka.
“Janyewar ‘yan sanda a irin wannan rana ta tarihi abu ne da ya nuna rashin kishin ƙasa, kuma ba za mu lamunci hakan ba,” in ji gwamnan.
Abba Kabir Yusuf, ya kuma bukaci shugaban kasa da ya sauke CP Bakori, du ba da cewa abinda ya aikata raini ne ga doka da ma al’ummar Kano baki daya.
Duk da haka, Yusuf ya gode wa sauran hukumomin tsaro da suka halarci taron, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa zaman lafiya da haɗin kai a Kano.

