Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sallami Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, daga muƙaminsa.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya naɗa Mustapha Bakwana a matsayin sabon Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Siyasa domin maye gurbin Sunusi Surajo Kwankwaso.

