Gwamnatin Jihar Bauchi na duba yiwuwar kafa doka da za ta hana mata haihuwa a gida, sakamakon karuwar haɗarin mutuwar uwa da jarirai. Rahoton UNICEF ya nuna cewa kashi 31 cikin 100 ne kawai ke haihuwa a asibiti, yayin da kashi 69 ke haihuwa a gida, duk da cewa da dama na halartar awo.
Masana kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki daga ma’aikatun gwamnati, majalisar dokoki, kananan hukumomi da kungiyoyin farar hula sun bayyana damuwa kan lamarin. A wani taron kwanaki biyu, wakilin UNICEF Oluseyi Olosunde ya bukaci ƙara kasafin kuɗi da gaggauta ɗaukar matakan rage mace-macen mata da jarirai a jihar.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin Farko ta Jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Mohammed, ya ce ana la’akari da doka da za ta tilasta halartar awo da haihuwa a asibiti, tare da hukunci ga masu karya dokar. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Suleiman, ya jaddada cewa majalisar za ta ɗauki matakin doka domin kare lafiyar mata da yara a jihar.

