Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da sabon aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, cikin Karamar Hukumar Balanga. Aikin dai haɗin gwiwa ne tsakanin Hukumar Samar da Wuta a Karkara (REA), Bankin Duniya da kamfanin MIDS Dynamics, wanda aka tsara zai kawo haske ga fiye da gidaje 8,000 a yankin da kewaye cikin watanni huɗu.
A bikin kaddamarwar, Gwamnan ya bayyana aikin a matsayin mataki mai muhimmanci wajen bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta da araha, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa. Ya ce wannan na daga cikin manufofin gwamnatinsa na inganta rayuwar jama’a, musamman mazauna karkara da suke fama da rashin ingantacciyar wuta.
Shugaban REA, Injiniya Abba Aliyu, ya yaba da hangen nesa da jajircewar Gwamnan, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta ƙaddamar da ƙarin ayyukan sola a wasu ƙananan hukumomin jihar. Shugaban kamfanin MIDS Dynamics, Injiniya Halis Mohammed, ma ya bayyana Gombe a matsayin jiha ta farko a Najeriya da ta bayar da kuɗin haɗin gwiwa don irin wannan gagarumin tsarin.
Shugabannin al’umma a Talasse sun nuna farin cikinsu tare da gode wa gwamnati bisa cika alkawarin da aka dade ana jira. Sun ce wutar lantarki za ta taimaka wajen dawo da kasuwanci, inganta zaman rayuwa, da rage dogaro da janareto da ya yi tsada. Sun kuma yi alƙawarin kula da kayan aikin don guje wa lalacewa da sata.

