Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhini da girgiza bisa rasuwar ‘yan majalisar dokokin jihar guda biyu, Hon. Sarki Aliyu da Hon. Aminu Sa’adu, da suka rasu a rana guda. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature, ya fitar a Kano ranar Alhamis, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin baƙin ciki mai girma a tarihin jihar.
Gwamna Yusuf ya ce mutuwar ‘yan majalisar biyu a lokaci guda ta jefa gwamnati da al’ummar Kano cikin jimami, inda ya bayyana su a matsayin jajirtattun wakilai da ke cike da kuzari da kishin jama’arsu. Ya ce wannan rashi abin tausayi ne da kalmomi ba za su iya misalta girman baƙin cikin da ya haifar ba.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, shugabanci da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, da kuma al’ummomin Kano Municipal da Ungoggo. Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya sanya su cikin rahamarSa, tare da bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano haƙurin jure wannan babban rashi, yana mai kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa, haɗin kai da addu’a.

