Gwamnatin Tarayya ta sanar da ayyana 25 da 26 ga Disamba, 2025 a matsayin hutun Kirsimeti da Boxing Day, yayin da ta ƙara da 1 ga Janairu, 2026 domin bikin Sabuwar Shekara a duk faɗin Najeriya.
Sanarwar ta fito ne daga Ma’aikatar Harkokin Ciki a ranar 22 ga Disamba, 2025, inda Ministan Harkokin Ciki, Olubunmi Tunji-Ojo, ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi anfani da wannan lokaci wajen tunani kan muhimmancin ƙauna, zaman lafiya da sadaukarwa a rayuwa.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba, da su yi addu’a domin ingantaccen tsaro da cigaban ƙasa, tare da bin doka da oda yayin shagulgulan bukukuwan.

