Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyar Sun Sace Mata Tara a Sokoto

      November 9, 2025

      Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Damuwa Kan Masu Satar Kayan Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano

      November 9, 2025

      INEC Ta Ayyana Soludo a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

      November 9, 2025

      An Yankewa Wasu Dillalan Miyagun Ƙwayoyi Hukuncin Shekaru 21 a Gidan Gyaran Hali

      November 8, 2025

      Ya Kamata Trump Ya Janye Kalamansa Sannan Ya Bawa Najeriya Haƙuri – Barau

      November 8, 2025
    • Siyasa

      INEC Ta Ayyana Soludo a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

      November 9, 2025

      An Rantsar Da Shugaban Ƙasa Mafi Tsufa a Duniya

      November 7, 2025

      Gombe Na Amfana Da Cire Tallafin Man Fetur – Inuwa Yahya

      November 4, 2025

      Sabon Rikici Na Shirin Kunno Kai Tsakanin Sanata Natasha Da Akpabio

      November 4, 2025

      Har Yanzu Bamu Janye Dakatarwar Shekaru 30 Da Mu Ka Yi Wa El-Rufai Ba – SDP

      November 2, 2025
    • Addini

      Ƙungiyoyin Fityanul Islam Da Samarin Tijjaniyya Sun Yi Ƙarar Gwamnatin Kano a Kotu

      November 5, 2025

      Saudiyya Ta Ragewa Najeriya Kujerun Hajjin 2026

      October 17, 2025

      Sarkin Musulmi Ya Buƙaci a Samar Da Dokokin Amfani Da Kafafen Sada Zumunta a Najeriya

      October 16, 2025

      Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Laifin Yin Aure Ba Tare Da Amincewar Iyayensu Ba

      October 13, 2025

      Tinubu Ya Bawa NAHCON Umarnin Rage Kuɗin Hajjin 2026 Cikin Gaggawa

      October 7, 2025
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021

      Popular New Xbox Game Pass Game Being Review Bombed With “0s”

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Damuwa Kan Masu Satar Kayan Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano
    Featured

    Gwamnatin Tarayya Ta Nuna Damuwa Kan Masu Satar Kayan Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanNovember 9, 2025No Comments2 Mins Read

    Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da yadda wasu mutane ke lalata aikin gina babban titin Abuja–Kaduna–Kano da ake ci gaba da yi. Karamin Minista na Ma’aikatar Ayyuka, Bello Muhammad Goronyo, ya bayyana haka yayin duba aikin a ranar Asabar, inda ya ce an samu rahotanni na wasu bata-gari da ke balle ƙarafa da sauran kayan aikin titi domin sayarwa.

    Goronyo ya bayyana cewa an ga misali a kusa da gadar Jaji a Kaduna, inda wasu masu sayen shara da ake kira Baba Bola suka kwashe sandunan ƙarfe daga sabbinn gadoji. Haka kuma, akwai wasu da ke amfani da sabon titin wajen busar da hatsi ko zubar da shara, da ma yin ramuka domin saka igiyoyin wutar lantarki ko ruwa.

    Ministan ya yi kira ga shugabannin al’ummomi da su fadakar da jama’arsu su daina irin waɗannan ayyuka da ke durƙusar da ci gaban aikin da gwamnati ta zuba kuɗi mai yawa a kan sa. Ya ce titin na da muhimmanci wajen rage lokacin tafiya, kara tsaron hanya da rage haɗura. Haka kuma, ya bayyana cewa tun fara aikin, matsalolin tsaro a hanyar suka ragu sosai.

    A nasa ɓangaren, Daraktan Hanyoyi na Ma’aikatar Ayyuka, Clement Ogbuagu, ya ce aikin na tafiya bisa tsari, inda ya tabbatar da cewa gwamnati da kamfanin mai aikin ba sa gajiya wajen tabbatar da kammala titin cikin lokaci. Ya bayyana aikin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan hanya da ke tafiya da sauri a ƙasar.

    Abuja–Kaduna–Kano
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleINEC Ta Ayyana Soludo a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
    Next Article Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyar Sun Sace Mata Tara a Sokoto
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyar Sun Sace Mata Tara a Sokoto

    November 9, 2025
    Featured

    INEC Ta Ayyana Soludo a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

    November 9, 2025
    Featured

    An Yankewa Wasu Dillalan Miyagun Ƙwayoyi Hukuncin Shekaru 21 a Gidan Gyaran Hali

    November 8, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202536 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202535 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202526 Views

    Matuƙar Ba’a Yi Yadda Aka Yi a Afghanistan Ba Baza’a Kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya Ba – Amurka

    November 6, 202522 Views

    Zama a Banɗaki Fiye Da Kima Kan Haifar Da Matsala Ga Lafiyar Ɗan Adam – Likita

    October 28, 202520 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2025 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.