Gwamnatin Tarayya ta ware sama da ₦49bn a kasafin kuɗin 2026 domin ciyar da fursunoni, samar da magunguna, tufafi, da kuma gyaran gidajen yari a faɗin ƙasar. Haka kuma an tanadi kuɗaɗe don sayen makamai da kayan tsaro.
Bayanin kasafin ya nuna cewa an ware ₦40bn don abinci, ₦1bn don tufafi, ₦1bn don magunguna, ₦5bn don gyare-gyaren gine-ginen gidajen yari, da kuma ₦861m don kayan tsaro da na’urorin tantance bayanai. Rahotanni sun nuna cewa yawan fursunoni a Najeriya ya kai 77,438, inda fiye da rabinsu ke jiran shari’a.
Ministan Harkokin Ciki, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa ana shirin sauya wuraren wasu gidajen yari domin sabuntawa, duba da cewa da dama daga cikinsu tsofaffi ne tun shekarun 1950. Ya ce wannan shiri na da nufin inganta tsaro, walwala da kuma gyaran tarbiyyar fursunoni a kasar.

