Aƙalla manoma biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutane da dama ciki har da yara suka jikkata sakamakon wani harin sama da aka kai a ƙauyen Kurgi da ke Karamar Hukumar Mariga a Jihar Neja. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, kamar yadda mazauna yankin suka shaida.
Rahotanni sun nuna cewa wani jirgin sojan sama mai aikin sa ido ya yi ta shawagi a saman ƙauyen na tsawon lokaci kafin ya buɗe wuta. Wani mazaunin yankin, Suleiman Sanusi, ya ce harsasan sun samu mutane a cikin gidajensu, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.
Sanusi ya bayyana harin a matsayin abin mamaki da ba tare da wani dalili ba, yana mai cewa hakan ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa garin Bangi da wasu wurare masu aminci. Ya buƙaci hukumomi da su gaggauta bincike tare da bai wa waɗanda suka jikkata kulawar lafiya, yayin da har yanzu rundunar sojin sama da sauran hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba.

