Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta kama direbobin motoci fiye da 250 a Babban Birnin Tarayya Abuja cikin kwanaki biyu, saboda karya dokar da ta tilasta ɗaukar mutum ɗaya ne kawai a kujerar gaba ta motar haya.
Kwamandan FRSC a FCT, Felix Theman, ya ce aikin ya fara ne a ranar 2 ga Oktoba domin rage cunkushe fasinjoji da tabbatar da tsaro a kan hanya.
Hukumar ta ce ɗaukar mutane biyu a gaba yana hana amfani da bel, yana lalata tayoyi da tsarin mota, kuma yana hana direba samun cikakken iko yayin tuki.
An gudanar da aikin ne tare da kungiyoyin direbobi da kotunan tafi-da-gidanka, inda aka gargadi masu amfani da tsofaffin motoci marasa tsaro da su sabunta su ko su fuskanci hukunci.

