Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da dage taron National Executive Committee (NEC) karo na103 da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025. Kakakin jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X ranar Litinin, inda ya ce hukumar gudanarwa ta jam’iyya ta yanke wannan shawara ne a wani taron gaggawa da ta gudanar a Abuja.
A cewar Ologunagba, kwamitin ya yi amfani da ikon da ke karkashin Sashe na 29(2)(b) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar (gyaran 2017) wajen dage taron zuwa wani sabon lokaci da za a sanar da mambobi nan gaba. Jam’iyyar ta bukaci dukkan mambobin NEC da su lura da wannan canji tare da jiran karin bayani daga sakatariyar jam’iyya ta kasa.
Dage taron ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar matsin lamba sakamakon ficewar wasu manyan ‘ya’yanta zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Wannan sauyin siyasa ya sanya jam’iyyar ke sake duba shirye-shiryenta na cikin gida kafin babban taron kasa.
Duk da haka, shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa ko sauya sheka ko tasirin waje ba zai iya dakatar da babban taron jam’iyyar ba. Ya tabbatar cewa taron kasa na PDP zai gudana kamar yadda aka tsara a Ibadan, Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.

