Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa ta fara tantance lafiyar maniyyatan da ke shirin aikin Hajjin shekarar 2026. An ƙaddamar da aikin ne a ranar Talata a Babban Asibitin Hadejia, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajjin.
Darakta Janar na hukumar, Umar Labbo, ya ce tantance lafiyar na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da lafiya da tsaron maniyyatan jihar. Ya bayyana cewa hukumar za ta bi ƙa’idojin Saudiyya, inda aka tanadi cewa sai wanda lafiyarsa ta ƙoshi ne kaɗai za a bari ya yi aikin Hajji.
Labbo ya ƙara da cewa hukumar za ta gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci, tare da kira ga maniyyata da su ba da haɗin kai ga jami’an lafiya. Ya jaddada cewa hukumar na yin duk mai yiwuwa domin ganin maniyyatan Jigawa sun shirya tsaf domin tafiyar Hajjin.

