Gwamnatin Jihar Bayelsa ta ce ta kammala sayen jirage biyu domin farawa da gudanar da jigilar kasuwanci daga filin jirgin sama na Bayelsa International Airport zuwa biranen Abuja da Legas.
Gwamna Douye Diri ne ya bayyana hakan a Yenagoa yayin wata ziyarar ban girma da Firayim Ministan ƙasar State of Africa in Diaspora, Dr Tin Louise-George, ya kai gidan gwamnati.
Gwamnan ya ce an ɗauki matakin ne don tabbatar da cewa filin jirgin saman jihar ya zama mai cikakken amfani, bayan matsalolin da aka samu a baya, wanda ya sa aka har aka rage zirga-zirgar jirage.
Ya ƙara da cewa jiragen da aka saya za su rika tashi kowace rana zuwa Abuja da Legas, tare da shirin faɗaɗa filin jirgin sama da kuma gina sabuwar “New Yenagoa Smart City”.
A nasa jawabin, Dr Louise-George ya nuna shirinsu na haɗin gwiwa da jihar wajen ci gaban harkar jiragen sama, ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa birnin zamani, yana mai cewa hukumar da yake jagoranta za ta samar da tallafi da saka hannun jari don inganta ayyukan.

