Fasto Tunde Bakare ya ce matsin lambar da Shugaba Donald Trump ke yi wa Najeriya, ciki har da sanya ta cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kanta, na da nasaba da son mallakar arzikin man ƙasarta. Ya bayyana haka ne a jawabinsa na State of the Nation a Citadel Church, inda ya ce Trump yana kallon man Najeriya, ma’adinai da harkar fasaha a matsayin muhimman ginshiƙai ga manufar kasarsa.
Bakare ya ce tun bayan nasarar Trump a zaben 2024, ya samu wani hangen nesa da ya nuna shugaban zai nuna ƙwarin gwiwa a kan Najeriya saboda sha’anin man fetur, siyasar Gabas ta Tsakiya da fasahohi masu tasowa. Ya kara da cewa wannan sha’awa na iya haifar da rikice-rikicen addini idan ba a sarrafa ta da hikima ba, inda ya yi nuni da cewa Trump dan kasuwa ne, don haka Najeriya ta je teburin tattaunawa da tsari mai amfani ga bangarorin biyu — inji shi.
Bakare, wanda ya yi tsokaci kan matsalar tsaro a bangarori da dama na Najeriya, ya ce abin kunya ne yadda wasu al’ummomi ke neman taimakon Amurka saboda gazawar gwamnati. Ya ambaci gwamnati da majalisar dokoki wajen magance kashe-kashe a Benue, Plateau, Kaduna da yankin Kudu maso Gabas, inda ya ce hatta Majalisar Amurka ta yi muhawara kafin ‘yan majalisar Najeriya su nuna damuwa.
A ƙarshe ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya zaɓi hanyar gyaran tsarin kasa maimakon shirin siyasa na 2027, tare da ɗaukar matakan gaggawa kamar kafa rajistar wadanda rikice-rikicen tsaro suka shafa, inganta rundunonin tsaro, kafa hukumar sasanci da sake tsari, da ba da dama ga sabon tsarin ‘yan sanda na jihohi da yankuna. Ya ce lokaci ya yi da Najeriya ta magance matsalolin da suka jima ana dannewa domin samun zaman lafiya mai dorewa.

