Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kamo wasu mutane biyar da ake zargi suna da alaƙa da fitaccen ɗan bindiga Bello Turji, bayan sun gaza halartar kotu domin fara shari’arsu. Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba, 21 ga Janairu 2026, da misalin karfe 4:35 na yamma.
Kotun ta amince da bukatar Lauyan Gwamnatin Tarayya na fitar da takardar izinin kamo mutanen, sakamakon rashin zuwansu kotu duk da kiran da aka yi musu. Wadanda ake zargin sun hada da Musa Kamarawa, Abubakar Hashimu (Doctor), Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma, inda lauyansu ya bayyana mamakinsa kan rashin bayyanarsu duk da alkawarin da suka dauka.
A rahoton da BechiHausako ke bibiyowa, an gurfanar da mutanen tun a watan Disamban 2024, bisa zargin taimaka wa kungiyoyin ’yan ta’adda da kayayyaki irin su kwayoyi, abinci, kakin sojoji da ’yan sanda, da kuma kayan gini zuwa sansanoninsu a jihohin Zamfara, Sakkwato da Kaduna.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu 2026, domin ci gaba da sauraron karar, yayin da hukumomi ke kokarin cafke wadanda ake zargin domin gurfanar da su gaban shari’a.

