Hukumar Nigerian Independent System Operator (NISO) ta bayyana cewa sama da kashi 68 cikin 100 na masu amfani da lantarki a Najeriya na satar wuta ta hanyar kauce wa amfani da na’urar prepaid meter ko kuma haɗa wuta kai tsaye ba tare da biyan kuɗi ba. Wannan jawabi ya fito ne a taron shekara-shekara na kungiyar manema labaran bangaren wutar lantarki, inda masana suka gargadi cewa matsalar satar wuta na kara tsananta gibin kuɗi a bangaren.
Shugaban Mainstream Energy Limited kuma memba a hukumar NISO, Audu Lamu, ya ce matsin tattalin arziki, tashin farashi, rashin aiki da ƙarancin karfin saye sun sanya mutane da dama kasa iya biyan kudin wuta, lamarin da ke ƙara yawan energy poverty. Ya ce dole a samar da farashi mai ma’ana (cost reflective tariff), amma ta hanyar da za ta kare talakawa ba tare da tura su cikin mawuyacin hali ba. Ya ba da shawarar tsarin tallafin da zai kasance karkashin tantance sahihan marasa karfi kawai, maimakon tallafin banbanci da yake ci gaba da haifar da almundaha.
Haka kuma, babban Manajan NISO, Ali Bukar, ya ce matsalar satar lantarki ta jawo karancin kudaden shiga, abin da ke barazana ga dorewar harkar samar da wuta. Ya bukaci a kara tsaurara hukunci ga masu satar wuta da kuma amfani da fasahohin zamani don gano masu karya haɗin lantarki da kauce wa mita.
Kungiyar PCAN kuma ta ce fiye da shekaru goma bayan kamfanonin wuta sun shiga hannun masu zaman kansu, har yanzu bangaren wutar Najeriya na fama da gibin kuɗi, ƙarancin iskar gas, tsofaffin kayayyakin rarrabawa da tsada a kasuwannin waje. Masana sun jaddada cewa ba za a warware matsalar ba sai an hada tsauraran matakan hana sata, tsarin farashi mai adalci, da ingantacciyar kula da masu ƙaramin karfi a lokaci guda.

