Majalisar Dattawan Najeriya ta ce za ta kammala gyaran Kundin Tsarin Mulkin 1999 domin bai wa jihohi damar kafa ‘yan sandansu kafin ƙarshen shekarar 2026. Kakakin majalisar, Yemi Adaramodu, ya shaida wa Punch Newspapers cewa za su fara aikin da zarar sun koma zama mako mai zuwa. Wannan na zuwa ne bayan buƙatar Shugaba Bola Tinubu na a saka batun ‘yan sandan jihohi cikin kundin domin magance matsalar tsaro.
Tinubu ya kuma buƙaci a tanadi kariya a cikin dokar domin hana gwamnoni amfani da rundunar ta jiha ba daidai ba. Adaramodu ya ce tuni aka gudanar da tuntuba a yankuna daban-daban, kuma kwamitin duba kundin ya tattara rahotanni kafin a dakata domin gyaran dokar zaɓe da kasafin kuɗin 2026. Ya tabbatar da cewa za a kammala aikin kafin fara kamfen ɗin zaɓe mai zuwa.
A halin da ake ciki, ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria da Afenifere sun goyi bayan shirin, amma sun nemi a sanya tsauraran matakan kariya domin hana cin zarafi. Shugaban MACBAN, Baba Ngelzarma, da kakakin Afenifere, Jare Ajayi, sun jaddada bukatar sa ido da dokokin da za su takaita yiwuwar amfani da rundunar wajen murƙushe abokan hamayya.

