Majalisar Wakilai ta Najeriya ta nuna ɓacin rai kan harin da aka kai wa tawagar dan majalisa, Jafaru Mohammed Ali, daga mazabar Borgu/Agwara a Jihar Nejar. Lamarin ya faru ne a kan hanyar Lumma–Babanna, lokacin da dan majalisar yake kan tafiya domin gudanar da aikin tuntubar mazabarsa.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi, ya fitar, an bayyana cewa harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu jami’an tsaro da ke cikin tawagar, yayin da direba da wasu daga cikin hadiman dan majalisar suka ji raunuka. Haka zalika, motocin tawagar da dama sun lalace sakamakon harin.
Majalisar ta jajantawa iyalan jami’an da suka rasu, tare da yi musu addu’ar samun rahama da gafara. Haka kuma ta yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, tare da rokon hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
A ƙarshe, Majalisar ta jaddada cewa wannan al’amari ya sake haskaka matsalar tsaro da ke addabar yankuna da dama a ƙasar, musamman yankunan kan iyaka. Ta ce za ta ci gaba da ba wa bangaren tsaro goyon bayan da ya dace, domin a kawo karshen ta’addanci, fashi da sauran laifukan da ke tayar da hankalin jama’a a Najeriya.

