Sabon rahoton Kididdigar Lafiyar Najeriya na 2025 ya nuna cewa mata masu juna biyu, jarirai, da yara ƙasa da shekaru biyar 20,811 suka rasu daga watan Janairu zuwa Satumba 2025. Rahoton, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fitar, ya ce Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen da ke fama da ƙaruwar mace-macen mata da yara saboda matsalolin samun kulawa ta gaggawa da ƙarancin kwararrun ma’aikatan lafiya.
A cikin watanni uku na farko, an tabbatar da mace-macen mata 1,244, jarirai 1,706, da yara ƴan ƙasa da shekaru biyar 3,820. A zango na biyu, mace-macen mata sun sauka zuwa 1,232, sannan a zango na uku sun kai 1,213. Sai dai mace-macen jarirai sun ƙaru daga 1,706 a zangon farko zuwa 1,900 a zangon uku, yayin da mace-macen yara ƴan ƙasa da shekaru biyar suka tashi daga 3,672 zuwa 4,215.
Rahoton ya bayyana cewa daga 2020 zuwa 2025, adadin mace-macen mata na sauyawa shekara-shekara. Mafi muni ya faru a 2021 da mace-macen mata 5,837, sannan ya ragu a 2023 zuwa 4,239, kafin ya ƙaru zuwa 5,391 a 2024. Shekara ta 2025 ta nuna raguwa mai yawa inda aka rubuta mace-mace 3,689 zuwa yanzu.
Abubuwan da suka fi haddasa mace-macen sun haɗa da rikice-rikicen juna biyu, cututtukan zuciya, ciwon sanyi, zazzabin cizon sauro, ciwon daji da HIV/AIDS. Ga jarirai kuwa, matsalolin haihuwa, asphyxia, kamuwa da cuta, ƙarancin nauyi, da tetanus sune manyan dalilai. Yara ƙasa da biyar kuma na mutuwa ne saboda zawo, malnutrition, ciwon huhu, meningitis, sepsis, da tetanus. Rahoton ya ce matsalar jinkirin neman kulawa da rashin ingantattun cibiyoyin lafiya na daga manyan matsalolin da ke jefa rayuka cikin haɗari.

