Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama da wuri a jihohin Kano da Neja da Ribas da wasu jihohi goma sha biyu.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata yayin ƙaddamar da hasashen yanayi na 2026.
Ya gargaɗi manoma da kada su yi gaggawar shuka, yana mai cewa duk da an fara samun ruwan sama a wasu wurare, ainihin kakar damina ba ta fara ba.
Ya kuma yi nuni da yiwuwar yanayi mai tsanani tsakanin watan Maris da Mayu na bana.
Rahoton NiMet ya nuna yiwuwar ruwan sama mai yawa a kudancin ƙasar, tare da fara damina da wuri a jihohi da dama, yayin da ake sa ran fara ta a makare a Borno.
Haka kuma, ana hasashen damina za ta ƙare da wuri fiye da yadda aka saba a wasu sassan jihohin Ogun da Osun da Ondo da Imo da Ribas da Akwa Ibom da Kogi da Neja.

