Rundunar ƴansandan Najeriya tare da haɗin gwiwar cibiyar yaƙi da laifukan intanet ta ƙasa (NPF–NCCC) ta bayyana cewa ta bankaɗo wata babbar ƙungiyar masu satar katin waya ta intanet da ta haddasa asarar kuɗi da ta haura naira biliyan 7.7. Ƙungiyar na karkatar da katin waya da bayanan intanet na wani kamfanin sadarwa ta haramtacciyar hanya.
Rundunar ta ce lamarin ya biyo bayan ƙorafin da kamfanin ya shigar, bayan lura da ayyukan zamba a tsarin biyan kuɗaɗe da lissafinsa. Bincike ya nuna cewa an sace bayanan wasu ma’aikatan kamfanin, abin da ya bai wa masu laifin damar shiga muhimman tsare-tsaren kamfanin ba tare da izini ba.
Bayan makonni na bincike, ƴansanda sun kai samame a jihohin Kano da Katsina a watan Oktoban 2025, tare da ƙarin kama wasu a Abuja, inda aka cafke mutum shida. An ƙwato gidaje biyu, ƙananan kantuna biyu, shagunan sayar da wayoyi da kwamfutoci, sama da kwamfutoci 400 da wayoyi 1,000, tare da gano kuɗaɗe masu yawa a asusun banki, yayin da ake shirin gurfanar da waɗanda ake zargi gaban kotu.

