Aƙalla ’yan bindiga 50 da ke addabar ƙananan hukumomin Musawa, Matazu da Danmusa a Jihar Katsina, tare da yankin Tsanyawa na Jihar Kano, ne suka mutu sakamakon harin sama da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta kai. Harin ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce an kai harin ne tare da goyon bayan wasu tsofaffin ’yan bindiga da suka tuba. Ya bayyana cewa waɗanda aka kashe wasu ne masu biyayya ga Baidu, wani shahararren jagoran ’yan bindiga da ke adawa da yarjejeniyar zaman lafiya a Danmusa da wasu sassan Katsina.
Danmusa ya ƙara da cewa an kashe ’yan bindigar ne a yankin Matazu yayin da suke dawowa daga hare-haren da suka kai a al’ummomin da ke kewaye da Tsanyawa a Kano. Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da ’yan bindiga, tare da tabbatar da cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro, al’umma da masu tuba na ci gaba da haifar da nasara a jihohin Kano da Katsina.

