Dakarun sojin Najeriya tare da jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda 12 tare da ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su a jihohin Zamfara, Sokoto da Gombe. Wannan nasara ta samu ne sakamakon hare-hare na hadin gwiwa da hukumomin tsaro ke ci gaba da kai wa, domin murkushe ayyukan ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
A Zamfara, dakarun Runduna ta 8 karkashin Operation Fansan Yamma, sun kai farmaki sansanonin ’yan ta’adda a dajin Sububu da ke Maradun, inda suka kashe shida tare da lalata sansanoninsu a yankunan Magaji, Galakaje, Filinga da Kukatara. Haka kuma, an kwato makamai da babura, tare da ceto wata yarinya ’yar ƙanana mai suna Halira Ibrahim da aka yi garkuwa da ita.
A Gombe kuma, jami’an ’yan sanda tare da mafarauta da ’yan sa-kai sun kashe ’yan bindiga uku tare da ceto mutane biyu a hare-haren da aka kai Rahama da Lambo a Karamar Hukumar Akko, sai dai mutum daya ya rasu. A Sokoto kuwa, jami’an tsaro sun tabbatar da ceto mutane hudu daga maboyar ’yan bindiga, inda hukumomi suka jaddada kudurinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

