Rundunar Sojin Najeriya ta musanta wani sako da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa za a aiwatar da umarnin “za a zauna a gida” a yankin Kudu-Maso-Gabas, inda ta bayyana sakon a matsayin karya da ayyukan ‘yan ta’adda.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojin Najeriya, 82 Division, Lt. Col. Olabisi Ayeni, ya ce manufar sako irin wannan ita ce tada tsoro da kawo cikas ga rayuwar jama’a. Kakaki24 ta samu bayanin cewa rundunar soji tare da sauran hukumomin tsaro sun riga sun kafa tsauraran matakan tsaro domin kare lafiyar mazauna yankin.
Ayeni ya jaddada cewa “’Yancin motsi da gudanar da ayyukan yau da kullum na mazauna yana nan, ba tare da wani tsangwama ba,” sannan ya gargadi duk wanda ya yi ƙoƙarin tilasta wannan umarni na bogi cewa za a hukunta shi. Rundunar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani yunkuri na tayar da hankalin jama’a da hana ci gaban al’umma, tare da ƙarfafa su da cewa “idan kun ga abin da ba daidai ba, ku bayyana.”
Ya ƙara da cewa ayyukan tattalin arziki za su ci gaba ba tare da wata tangarda ba, kuma duk wanda ya yi ƙoƙarin amfani da ƙarfi wajen aiwatar da umarnin bogi zai fuskanci hukunci mai tsanani.

