Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyya ta Tarayya da ke Azare, Jihar Bauchi, zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, domin girmama fitaccen malamin addinin Musulunci wanda ya rasu a baya-bayan nan. Shugaban ya sanar da hakan ne, yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar Bauchi, inda ya yi addu’a ga marigayi malamin tare da jajanta wa iyalansa da mabiyansa.
Tinubu ya samu tarba daga Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, tare da wasu gwamnoni, ministoci da manyan jami’an gwamnati bayan isowarsa filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa. A jawabinsa, gwamnan ya yaba da matakin shugaban ƙasa, yana mai bayyana shi a matsayin girmamawa ga Bauchi da Najeriya baki ɗaya, tare da jaddada rawar da Sheikh Dahiru Bauchi ya taka wajen inganta zaman lafiya, hakuri da fahimtar juna tsakanin addinai.
Bechi Hausa ta ruwaito cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kasance jagoran darikar Tijjaniyya, kuma malami ne da aka san shi a fadin Afirka ta Yamma saboda gudunmawarsa a fagen ilimi da addini. Gwamnan Bauchi ya bayyana rasuwarsa a ƙarshen watan Nuwamba a matsayin babban rashi ga ƙasa, yana mai cewa sauya sunan jami’ar wata hanya ce ta ɗorewa wajen tunawa da rayuwarsa da ayyukansa na alheri.

