Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce dole ne a gyara abubuwan da ba sa aiki a ƙasar tare da haɗin kan ‘yan ƙasa domin samar da ci gaba da tsaro. Ya bayyana hakan ne a walimar buɗe baki da ya shirya wa gwamnoni da manyan jami’an gwamnati a fadar shugaban ƙasa.
Tinubu ya ce wajibi ne a nuna ƙarfin hali wajen gyara matsaloli tare da haɗa kai domin kare martabar ƙasa. Ya kuma bayyana shirin kafa ‘yansandan jihohi domin magance matsalolin tsaro, yana mai cewa tsaro shi ne ginshiƙin bunƙasar noma, kasuwanci da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Haka kuma, shugaban ya buƙaci gwamnoni su ƙara ƙaimi wajen ayyukan jin kai a watan Ramadan, musamman ga matasa, mata da al’ummomin ƙananan hukumomi. Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da cika alkawuran da ta ɗauka, tare da samar da fata da tsaro ga ‘yan ƙasa.

