Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ajiye aikinsa kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa BBC. Majiyar ta ce ya sauka daga muƙaminsa ne a ranar Talata.
Har yanzu rundunar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin. Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan shugabancin rundunar, ba tare da cikakken bayani kan dalilin saukar tasa ba.
A watan Yunin 2023 ne shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sanar da shi domin naɗa shi muƙamin. Daga baya Majalisar ‘yan sandan ƙasar ta tabbatar da naɗin nasa a ƙarshen watan Oktoban shekarar 2023.

