Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar kawo karshen ta’addanci a Najeriya tare da inganta hulda ta diflomasiyya da sauran kasashen duniya. Ya bayyana haka ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a Fadar Aso Rock, Abuja, ranar Alhamis 06 ga Nuwamba, wanda shi ne karo na farko tun watan Yuli.
Tinubu ya ce duk da kalubale da ake fuskanta, gwamnati na gudanar da tattaunawa da manyan kasashe domin tabbatar da tsaro, ci gaba da kwanciyar hankali da kuma habaka tattalin arzikin kasa. Ya kara da cewa nasarar Eurobond din dala biliyan 2.3 da aka fitar wadda aka nuna sha’awarta fiye da yadda ake bukata, na nuna yadda kasashen duniya ke da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin Najeriya.
Wannan jawabi na Tinubu ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu “damuwa ta musamman” kan batun tsaro, wanda gwamnatin Najeriya ta bayyana a matsayin rashin cikakken fahimta kan halin da ake ciki a kasar.
Shugaban ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa kasa mai dunkulewa, kana ya yaba wa ministocinsa da jajircewarsu wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Renewed Hope Agenda, tare da bukatar su ci gaba da aiki cikin hadin kai da tsantsar mayar da hankali.

