Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin taimakawa wajen kwantar da tarzoma da ta biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a ƙasar a daren Lahadi. Sanatocin sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin, suna mai cewa kare zaman lafiya a yankin lamarin da ya shafi kasashen makwabta baki ɗaya ne.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana wannan mataki a matsayin abin da ya dace a wannan lokaci, yana jaddada cewa duk wata barazana ga zaman lafiyar wata ƙasa makwabciya na iya shafar tsaron yanki baki ɗaya. Ya kuma ce haɗin kan kasashen yammacin Afirka na da matuƙar muhimmanci wajen kare dimokraɗiyya da hana taɓarɓarewar tsaro.
A cewar rahotannin da Bevhi Hausa ta tattara, Shugaba Tinubu ya aikewa da majalisar wasiƙa wacce aka karanta a zauren majalisar, inda ya bayyana cewa gwamnatin Benin ta bukaci taimakon jiragen sama na musamman daga rundunar sojin Najeriya bayan da wasu dakarun soji suka yi yunkurin hambarar da Shugaba Patrice Talon. Yunkurin dai ya haɗa da kutsa gidan talabijin na ƙasar domin sanar da tsige shugaban.
Shugaba Tinubu ya gargadi majalisar cewa Benin na fuskantar yunƙurin kwace mulki “ba bisa ka’ida ba” wanda ka iya ruguza cibiyoyin dimokraɗiyyar ƙasar. Wannan matakin tura sojoji na Najeriya na zuwa ne a lokacin da ECOWAS da sauran ƙasashen yanki ke ƙoƙarin hana yaduwar juyin mulki a yankin Afrika ta Yamma.

