Lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam kuma Babban Lauya a Najeriya (SAN), Femi Falana, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sanya doka da za ta hana yara ƙasa da shekara 16 amfani da kafafen sada zumunta. Falana ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2025, yayin taron farko na gasar muhawara ta Dare2Debate da aka gudanar a birnin Legas, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen kare lafiyar yara a zamanin da fasahar zamani ke tasiri sosai.
Falana ya ce a duniya ana ta muhawara kan illar kafafen sada zumunta ga matasa, inda ya bayar da misalin Australia wadda ta hana yara ƙasa da 16 amfani da su. Ya ƙara da cewa Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai bin sawun ƙasashen yamma, na iya ɗaukar irin wannan mataki nan gaba. A cewarsa, wajibi ne a tsara dokoki domin kare muradun yara. Haka kuma ya yi tsokaci kan talauci da rashin aikin yi, yana mai cewa su ne manyan dalilan da ke tura wasu matasa aikata laifuka, ba wai ‘yan Najeriya masu dabi’ar aikata laifi ba ne.
