Wani babban jigo a jam’iyyar APC, Henry Idahagbon, ya ce tsarin siyasar uban gida wata mummunar ƙirƙira ce ta ’yan siyasar Najeriya da ya kamata a rushe ta. Idahagbon, wanda ke wakiltar jihohin Edo, Ekiti da Ondo a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
Ya ce duk da cewa a kasashen duniya ana da manyan ’yan siyasa masu tasiri, babu inda siyasar uban gida ke lalata dimokuraɗiyya kamar a Najeriya. Ya ambaci jihohin Rivers da Edo a matsayin wuraren da aka fi ganin mummunan tasirin tsarin, yana tuno rikicin da ya faru tsakanin Godwin Obaseki da Adams Oshiomhole a lokacin mulkinsu.
Idahagbon ya jaddada cewa ya kamata duk shiugaban da ya kammala waadinsa ya hakura, ba tare da ƙoƙarin zaɓen magajinsu ba. Ya ce ya kamata Najeriya ta rungumi tsarin “mutum ɗaya, ƙuri’a ɗaya” tare da yin watsi da siyasar uban gida, yana mai cewa hakan na da illa ga siyasa da tafiyar dimokuraɗiyyar ƙasa.

