Hukumomin Jihar Plateau sun tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a ƙananan hukumomi bakwai, inda aka samu mutum 11 da aka tabbatar sun kamu, yayin da mutum huɗu suka rasu tun daga watan Disambar 2025. Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Nicholas Baamlong, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Jos.
A cewarsa, an fara gano cutar ne a ranar 20 ga Disamba, 2025 daga ƙaramar hukumar Quanpan, lamarin da ya sa gwamnati ta gaggauta kafa tawagar kula da annoba. Ya ce an gano mutane 109 da suka yi hulɗa da masu cutar, yayin da ake ci gaba da bibiyar su da kuma binciken sabbin masu alamun cutar.
An samu mutuwar mutane huɗu a manyan asibitocin jihar, ciki har da likita ɗaya da ya kamu da cutar yayin da yake kula da mara lafiya. Gwamnatin jihar ta ce an rarraba magunguna da kayan kariya a asibitoci, tare da ƙarfafa wayar da kan jama’a domin dakile yaɗuwar cutar a fadin jihar.

