’Yan sanda sun tabbatar da harin da aka kai wa Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Comprehensive da ke Maga, Jihar Kebbi, inda aka kashe Mataimakin Shugaban makarantar tare da jikkata shugaban makarantar yayin da yake ƙoƙarin kare dalibansa. Maharan, waɗanda suka tsallaka katangar makarantar da safiyar Litinin, sun yi harbe-harbe sannan suka yi garkuwa da dalibai 25 daga dakunan kwanan su.
Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa an tura rundunonin ’yan sanda waɗanda suka yi artabu da maharan, amma tuni suka tsere da waɗanda suka sace. Gwamnatin jihar ta aika da Mataimakin Gwamna, Sanata Umar Tafida, don duba halin da ake ciki, kasancewar Gwamna Nasir Idris na wajen jihar. Wannan hari ya zo ne a wani lokaci da yankin Maga ke fama da yawan hare-haren ’yan bindiga a kwanakin baya.
Mazauna yankin sun nuna bakin cikinsu kan lamarin, musamman ganin yadda aka kashe jami’in makarantar da kuma yadda aka sace dalibai ba tare da wata ƙwakkwaran kariya ba. Aliyu Yakubu, wani mazaunin Maga, ya shaida cewa harin ya faru ne ba tare da wani martani ba a farko, yana mai cewa abin da ya faru babban rashi ne ga makarantar da al’ummar yankin gaba ɗaya.

