Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da kama mutum goma da ake zargi da aikata ta’addanci da rikice-rikice a garuruwan Minna da Kontagora, tare da gano makamai masu haɗari da miyagun kwayoyi a hannunsu. Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar a Minna.
A cewar Abiodun, jami’an da ke aiki a ofishin ‘A’ Division na Kontagora sun kai samame a yankin Tudun-Wada ranar 23 ga Oktoba, inda suka kama mutane uku — Abdullahi Abdullahi (22), Fahad Abubakar (19), da Nasiru Aliyu (28). An ce an same su da tabar wiwi mai yawa, wukake guda biyu, da kuma wandon soja, inda ake ci gaba da bincike a kansu.
Haka kuma, jami’an da ke ofishin ‘yan sanda na Central Police Station Minna sun kai farmaki a wuraren da ake zargin ɓarayi da masu ta’addanci ke ɓuya, ciki har da Angwan Sarki, Kuta Road, Sabon-Gari, Ogbomosho, Baida, da Makera. A wannan samame, an kama mutane bakwai da suka haɗa da Hamza Dauda (28), Hussain Sanda (25), Sani Hassan (22), Danlami Garba (25), Saidu Hassan (19), Musa Umar (21), da Hassan Usman (25).
Abiodun ya ce an kama waɗannan mutanen ne da tabar wiwi, shisha, da wasu abubuwan maye, kuma tuni an gurfanar da su a kotu ranar 24 ga Oktoba. Ya ce rundunar za ta ci gaba da kai samame a duk inda ake samun bayanai kan ‘yan daba da masu tada zaune tsaye domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

