Hukumomin tsaro a ƙasar Libya sun kama wasu ‘yan Najeriya biyu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi. Rahotanni daga shafin sa ido kan ‘yan gudun hijira, Migrant Rescue Watch, sun nuna cewa an cafke mutanen ne a birnin Zliten yayin da suke da tarin kwayoyi na hashish da allurai masu sa maye, waɗanda aka tanada domin rarrabawa.
Bayanan hukumomi sun ce rundunar ‘yan sanda ta musamman (CID) ce ta kama su, kuma an same su ba tare da takardun izinin zama ba. Daga bisani an mika su ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban kotu.
Wannan ba shi ne karo na farko da hukumomin Libya ke kama ‘yan Najeriya da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ba. A watan Yuli, rundunar yaƙi da ta’addanci ta kasar ta kama wasu ‘yan Najeriya biyu bisa zargin irin wannan laifi.
Masu lura da harkokin ƙaura sun bayyana damuwa cewa irin waɗannan ayyuka na bata sunan Najeriya a idon duniya, tare da ƙara tsananta kallon da ake yi wa ‘yan kasar a ƙasashen waje.

