An rawaito cewa rundunar sojin Amurka ta tsara yiwuwar kai hare-haren sama a Najeriya sakamakon umarnin da Shugaba Donald Trump ya bai wa Ma’aikatar Tsaron ƙasar, domin kare Kiristoci daga hare-haren ta’addanci. Rahoton jaridar New York Times ya ce an gabatar da zaɓuɓɓuka uku ga ma’aikatar tsaro: na “mai nauyi”, wanda zai haɗa da tura jiragen yaki da tawagar jirgin ruwa a Gabar Tekun Guinea; na “matsakaici” da ke amfani da jiragen yaki marasa matuki wajen kai hare-haren cibiyoyin ‘yan ta’adda; da na “mai sauƙi” da ke takaita kai tsaye ga musayar bayanan tsaro da tallafin leƙen asiri.
Sai dai jami’an soja a Pentagon sun ce ko da Amurka ta kai hare-haren sama, hakan ba zai kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya ba muddin ba a tsaya kan faɗa mai zurfi kamar yadda aka yi a Afghanistan ko Iraq, wanda a cewar rahoton babu wanda ke goyon bayansa a Washington a yanzu. A baya dai Trump ya yi barazanar tura sojojin Amurka Najeriya domin dakatar da abin da ya kira “kisan gilla ga Kiristoci”, lamarin da gwamnatin Najeriya ta musanta tana mai cewa matsalar ba ta addini bace, illa matsalar ta’addanci da ta shafi kabilu da al’ummomi da dama.
A gefe guda, kasar China ta nuna goyon bayanta ga Najeriya, tana mai cewa ba ta amince da kowacce ƙasa ta shiga harkokin cikin gida na wata ƙasa karkashin sunan kare addini ko ‘yancin dan Adam ba. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Mao Ning, ta ce kasar na goyon bayan ‘yancin Najeriya da bin hanyoyin diflomasiyya wajen magance matsalolin tsaro.
Gwamnatin Najeriya ta nanata cewa tun daga shekarar 2023 ana samun ci gaba wajen yaki da ta’addanci, inda ta ce an hallaka sama da mayaka 13,500 tare da ceto mutane fiye da 11,000 da aka yi garkuwa da su. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnati na kare ‘yan ƙasa ba tare da bambancin addini ba, tana kuma maraba da haɗin gwiwa da Amurka matuƙar an mutunta ikon Najeriya a kan yankinta.

