Wasu jami’an soji a Guinea-Bissau sun bayyana cewa sun karɓi cikakken iko a kasar, a daidai lokacin da ake samun rahotannin kama shugaban ƙasa Umaro Sissoco Embaló. Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan an ji ƙarar harbe-harbe a Bissau, babban birnin ƙasar, inda majiyoyin gwamnati suka tabbatar da cewa an tsare shugaban. Sojojin sun bayyana a gidan talabijin na ƙasa, suka sanar da dakatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Lahadi, wanda ya kasance cikin takaddama tun kafin kada kuri’u.
Sojojin sun bayyana cewa za su ci gaba da tafiyar da harkokin ƙasar bayan dakatar da tsarin zabe da suka zargi da rashin gaskiya, inda suka nuna cewa an hana dan takarar adawa shiga zaben. Kasar ta yi shirin sanar da sakamakon a ranar Alhamis, yayin da Embaló da abokin hamayyarsa Fernando Dias suka yi iƙirarin nasara kafin kammala ƙidaya. Janar Denis N’Canha, shugaban sojojin fadar shugaban ƙasa, ya karanta sanarwar da ta ayyana kwace mulki tare da rufe iyakokin Guinea-Bissau gaba ɗaya.
Kakaki24 ta tattaro cewa Janar N’Canha ya umurci al’ummar kasar da su kwantar da hankali, yayin da rahotanni ke nuna cewa baya ga shugaban ƙasa, an kuma kama hafsan sojojin shugaban ƙasa da wasu ministoci. Wannan mataki ya sake tayar da hankula a yammacin Afirka, yankin da ya sha fuskantar juyin mulki a shekarun baya, ciki har da Mali, Burkina Faso, Nijar da Gabon, lamarin da ke kara tursasa damuwa kan matsayin dimokuradiyya a nahiyar.
Masu sharhi na ganin cewa rikicin siyasa da rashin yarda kan sakamakon zabe na iya kara dagula lamarin a kasar da ta daɗe tana fama da rikice-rikicen siyasa. Har yanzu babu cikakken bayani game da yanayin da Embaló ke ciki, ko matakin da kungiyoyin yanki irin su ECOWAS za su ɗauka. Ana sa ran karin haske kan lamarin cikin sa’o’i masu zuwa, yayin da kasashen duniya ke kira da a mutunta doka da ‘yancin zabin jama’a.

