Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce cutar sankarar mahaifa cuta ce da za a iya rigakafinta kuma a warkar da ita idan aka samu damar yin gwaje-gwaje, allurar rigakafi da kuma magani yadda ya kamata. UN ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, inda ta ce kansar mahaifa ita ce cuta ta da mata suka fi kamuwa da ita a duniya.
Rahoton ya nuna cewa cutar na tasowa ne a mahaifar mace, kuma tana iya bazuwa zuwa wasu sassan jiki idan ba a gano ta da wuri ba. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a shekarar 2022, an gano mata kusan 660,000 da cutar, yayin da kimanin 350,000 suka mutu sakamakonta a faɗin duniya.
WHO ta jaddada cewa kusan dukkanin cutar na da alaƙa da kwayar cutar HPV da ake ɗauka ta hanyar jima’i, inda ta ba da shawarar a yi wa ’yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 allurar rigakafi, sannan mata su fara gwajin tantancewa daga shekara 30. Duk da haka, rashin daidaiton samun magani da rigakafi na ƙara haddasa mace-mace musamman a yankunan Afirka ta Kudu da Sahara.

