Jam’iyyar APC mai mulki ta samu gagarumar nasara a Majalisar Wakilan Tarayya bayan da wasu ‘yan majalisa guda shida suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar a ranar Alhamis. Wannan sauyi ya zo ne makonni kaɗan bayan da APC ta samu irin wannan rinjaye a Majalisar Dattawa, abin da ya ƙarfafa tasirinta a majalisun dokoki na ƙasa.
Cikin sabbin ‘yan majalisar da suka koma APC akwai ‘yan jam’iyyar PDP guda biyar daga Jihar Enugu da kuma ɗan jam’iyyar Labour Party ɗaya daga Jihar Filato. Wannan mataki ya baiwa APC damar mallakar kujeru 243 cikin 360 da ke majalisar, wanda ya zarce adadin da ake buƙata don samun rinjaye na kashi biyu cikin uku.
Sabbin alkaluman sun nuna cewa PDP yanzu tana da kujeru 72, LP kujeru 21, NNPP 15, APGA 5, ADC 1, SDP 2, yayin da YPP ke da kujera guda. Wannan ya nuna raguwar ƙarfin jam’iyyun adawa a majalisar, wanda a baya suka taɓa riƙe rinjaye a farkon zaman majalisar a shekarar 2023.
A watan Yunin 2023, APC na da kujeru 175 kacal, yayin da jam’iyyun adawa suka tara 182. Amma bayan shekara guda na sauye-sauye da sauya sheƙa daga wasu ‘yan majalisa, jam’iyyar ta mai mulki ta karfafa matsayinta, tare da samun cikakken rinjaye a majalisun dokoki na ƙasar.

