Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kammala rajistar zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Adamawa a ranar Litinin, matakin da ya ƙara hura wutar tasirin adawar Najeriya yayin da zaben 2027 ke matsowa kusa. Taron rajistar ya ja hankalin magoya baya da dama, inda gungun jama’a ke raye-raye, busa ganguna da ɗauke da hotunansa.
Wannan mataki ya zo ne bayan sanarwar da Atiku ya yi wa magoya baya a karshen mako, lamarin da ya tabbatar da bayyananniyar dawowarsa cikin harkokin siyasar adawa bayan fitarsa daga PDP. Mataimakisa kar harkokin yada labarai, Abdul Rasheeth, ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da bidiyo ya nuna motocin Atiku suna isa garin tare da tarbar jama’a cikin murna da ihu.
A rubutun da ya wallafa a shafinsa na X bayan rajistar, Atiku ya rubuta: “It’s official. -AA”, alamar tsayar da shawara kan sabuwar tafiyarsa. Wannan mataki, kamar yadda majiyoyi suka bayyana wa Kakaki24, zai ƙara wa ADC ƙarfi musamman ganin cewa Atiku ya taɓa ba da shawarar kafa gamayyar adawa tare da Peter Obi da Babachir Lawal tun a watan Yuli.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan sabon mataki zai ciyar da ADC gaba, tare da ƙara haɗa kan manyan ’yan adawa domin kalubalantar gwamnati mai ci a zaben 2027. Masu sharhi sun ce rajistar Atiku na iya zama babban tasiri ga yadda jam’iyyar za ta yi shiri da kuma rawar da za ta taka a babban zaben da ke tafe.

