Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da duk wasu da ake zargin za su bi shi zuwa jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bisa ra’ayinsu na kashin kansu. Ya ce shugabancin NNPP na jiha da ƙasa, tare da Jagoran jam’iyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba su amince da irin wannan sauya sheƙa ba. Dungurawa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, ranar Litinin, da safe.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin gwamnan da magoya bayansa sun janye wannan yunƙuri, domin mutunta jam’iyyar da kuma jama’ar Kano da suka ba su amana. A cewarsa, duk da roƙe-roƙe da nasihohi da aka yi, abubuwa sun ƙi juyawa, abin da ya sa ake ta yaɗa jita-jitar sauya sheƙar.
Dungurawa ya sake roƙon gwamnan da masu shirin bin sa da su sake tunani, su “mayar da wuƙarsu kube,” su tsaya kan NNPP maimakon komawa jam’iyyar APC wadda ya ce jama’a da masu zaɓe sun yi watsi da ita. Ya yi wannan kira ne a madadin shugabanni da magoya bayan jam’iyyar baki ɗaya.
Daga ƙarshe, shugaban NNPP na Kano ya karyata jita-jitar da ke alaƙanta shi da wasu jiga-jigan jam’iyyar da zargin haɗa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Jagora Sanata Kwankwaso. Ya ce shi, mataimakin gwamna, Sanusi Surajo, Sanata Rufai Hanga da sauran su ba su taɓa haɗa kowa da jagora ba, yana mai kalubalantar duk mai iƙirarin haka da ya fito da hujja.

