Layin wutar lantarki na ƙasa (National Grid) ya rushe a ranar Litinin, inda hakan ya jefa sassa da dama na Najeriya cikin duhu. Rahotanni sun nuna cewa rushewar ta faru ne sakamakon katsewar wuta daga manyan tashoshin lantarki, lamarin da ya yi sanadiyyar ɗaukewar wutar lantarki a jihohi da dama na ƙasar.
Bincike ya nuna cewa grid ɗin ya fadi ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana, bayan da yawan wutar da ake samarwa ya ragu matuƙa. Tun da farko a ranar, samar da wuta ya kai kusan megawatt 4,800, sai dai zuwa lokacin da lamarin ya faru, ya fadi ƙasa zuwa megawatt 139 kacal.
Har yanzu ba a san dalilin da ya haifar da matsalar ba, amma lamarin ya zo ne a daidai lokacin da Hukumar Kula da Tsarin Lantarki mai zaman kanta ta Najeriya ke ƙoƙarin ƙara samar da wuta bayan ƙalubalen ƙarancin iskar gas da ya samo asali daga lalata bututun mai. A lokacin da ake rubuta rahoton.

